IOC: An bukaci hana Rasha da Belarus shiga wasannin Olympics

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar shirya wasannin Olympics ta duniya ta bukaci a dakatar da kasashen Rasha da Belarus daga shiga duk wata gasar tsalle-tsalle ta duniya.
Sanarwar ta IOC ta kara da cewa gwamnatoci a Rasha da Belarus sun keta sharuddan ''Yarjejeniyar Olympics'', a kan haka IOC ke bukatar a dakatar da yan wasa daga kasashen shiga wasanni.
IOC ta kuma ce idan akwai yarjejeniya da wasu kungiyoyin inda ba zai yiyu a dauki irin wannan mataki ba, to yan kasashen za su iya shiga gasa a kashin kansu ba tare da inkiya da wata kasa ba.
Matakin na zuwa yayin da ake ci gaba da yaki a Ukraine bayan kutsen da Rasha ta yi a ranar Alhamis da ta gabata.
Kazalika zai shafi makomar kasashen da yan wasansu a gasar Olympics ta masu nakasa ta 'Winter Paralympics 2022' da za a fara a Beijing ranar Juma'a.
A ranar Lahadi itama Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta fada wa Rasha cewa za ta buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya amma da sunan 'Football Union of Russia', saboda kutsawa Ukraine da ta yi.
Hakama FIFA ta ce ba za ta yi amfani da tutar Rasha ko rera taken kasar ba, kuma zata buga wasannin ne a wata kasa daban.
To amma tuni kasashe da dama sun bayyana cewa ba za su buga wasa da Rasha ba, kuma matakin na FIFA bai yi tsauri ba.



























