Rikicin Ukraine: IPC ta hana Rasha da Belarus zuwa gasar masu nakasa a Beijing

Paralympian
An wallafa

Hukumar shirya gasar Olympics ta masu nakasa ta dakatar da yan wasan Rasha da Belarus daga halartar gasar Winter Paralympics da za a fara ranar Juma'a a Beijing.

A baya IPC ta aminta su shiga gasar ta masu nakasa a karan kansu, amma kuma bayan fuskantar suka daga kasashen Turai a yanzu ta sauya matsayarta.

A cewar Shugaban hukumar yan wasa da dama daga wasu kasashe sun ce ba za su shiga gasar ba matsawar aka kyale takwarorinsu daga kasashen Rasha da Belarus shiga.

A kan haka ya ce yan wasan Rasha da Belarus su yi kuka da gwamnatocinsu bisa wannan mataki.

A ranar Laraba ne Mr Parsons ya bayyana cewa dokar IPC ta ba yan wasa damar shiga gasar a kashin kan su ba tare da alakanta kan su da wata kasa ba.

To amma kuma matsin lamba ya sa hukumar ta dauki matakin dakatar da yan wasan daga zuwa Beijing.

''Mun yi imani cewa ba dai-dai bane a cakuda sha'anin wasanni da siyasa, to amma ta bayan fage kasashe da dama na da karfin fada a ji kan abinda ya shafi wasannin.'' In ji Parsons.

Hukuncin na IPC zai shafi yan wasa 71 daga Rasha da kuma 12 daga Belarus hadi da tawagoginsu.

Hukumomin kwallon kafa na Fifa da Uefa ne suka fara dakatar da Rasha da kungiyoyinta daga halartar duk wata gasa ta kwallon kafa saboda yakin Ukraine.