Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Wijnaldum, Suarez, Kean, Diaby, Deulofeu, Haaland, Martinez

k
An wallafa

Aston Villa na zawarcin ɗan wasan Paris St-Germain da ke buga tsakiya Georginio Wijnaldum kuma an shaida mata cewa za a sayar da ɗan wasan, mai shekara 31, a kan kimanin £21m. (Sport, via Sun)

Luis Suarez zai yi ban-kwana da Atletico Madrid idan kwantiraginsa ya ƙare a wannan kakar, kungiyar Italiya ta Inter Milan da Ajax, Sevilla da wasu na Brazil da ake cewa sun matsu dan wasan mai shekara 35 ya dawo garesu. (Marca - in Spanish)

Newcastle a shirye take ta mika tayin £50m kan ɗan wasan Bayer Leverkusen Moussa Diaby mai shekara 22, wanda darajarsu ta yi kasa idan aka kwatanta da £75m da ake biyansa. (Mail)

Paris St-Germain na nuna zawarcinta kan sake dauko ɗan wasan Everton Moise Kean, wanda ke zaman aro a Juventus zuwa kakar 2023. (Calciomercato - in Italian)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya musanta cewa kungiyar ta soma tattaunawa da Borussia Dortmund kan Erling Braut Haaland. (Goal)

Thomas Ricketts, mallakin babbar kungiyar league ta kwallon hannu Chicago Clubs, da hamshakin ɗan kasuwa Nick Candy sun kasance wanda ake alakantawa da yiwuwar saye Chelsea bayan mai kungiyar Roman Abramovich ya saya ta a kasuwa. (Sun)

Hamshakai kusan 10 wanda akasarinsu suka fito daga Amurka aka bayyana cewa sun mika tayinsu na mallakar Chelsea.(Sky Sports)

Wakilin Lautaro Martinez, Alejandro Camano ya kawo karshen jita-jitar da ake yaɗawa kan ɗan Argentina da ake cewa zai koma Arsenal, ya jadada cewa matashin mai shekara 24 zai ci gaba da zama a San Siro. (Calciomercato - via Football London)

Manchester United ta amince da yarjejeniyar saye Toby Collyer ɗan shekara 18 da ke buga tsakiya bayan gasa daidaita wa kan sabon kwantiragi da Brighton.(Mail)

West Ham ta gabatar da tayi mai kwaɓi kan ɗan wasan Udinese Gerard Deulofeu, wanda kuma ake ganin akwai yiwuwar ya komaAC Milan.(Calciomercato - in Italian)

KocinValencia Jose Bordalas ya ce za ta yi murna idan ɗan wasan Tottenhammai shekara21 Bryan Gil zai tsawaita zaman aron da ya ke da su wanda ke karewa a karshen kaka. (El Mercantil Valenciano - via Sport Witness)

Wigan Athletic da Blackburn Rovers na sanya ido kan ɗan wasan mai shekara 18 Ingila Josh Stones, wanda ke taka leda a Guiseley. (Sun)

Inter Milan ta tuntubi wakilin Paulo Dybala na Argentina, wanda kwantiraginsa da Juventus ke gab da karewa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)