Lille vs Chelsea: Watakila Azpilicueta da Alonso su buga fafatawar

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta ziyarci Faransa, domin buga wasa na biyu na zagaye na biyu a gasar Champions League da za su kara ranar Laraba.
Tuni koci Thomas Tuchel ya ce mai tsaron baya Cesar Azpilicueta da Marcos Alonso sun kammala shirin fuskantar kungiyar Faransa.
Kyaftin Azpilicueta ya murmure daga rashin lafiya, shi kuwa Alonso ya warke bayan jinyar cutar korona.
Sai dai kuma Tuchel ya ce da kyar ne idan Callum Hudson-Odoi da kuma Reece James za su iya buga karawar.
'Yan wasan biyu ba su yi wa Chelsea karawar Premier League da ta ci Newcastle 1-0 ranar Lahadi.
Chelsea ce ta yi nasara a kan Lille da ci 2-0 a wasan farko da suka kara a gasar a Stamford Bridge, inda Kai Havertz da Christian Pulisic suka ci kwallayen.
Gwamnatin Burtaniya ta samar da wani lasisi na musamman don ci gaba da gudanar da Chelsea, bayan da aka rufe asusun mai kungiyaer, Roman Roman Abramovich, wanda ake alakanta shi da amini ga ga shugaban Rasha, Vladimir Putin.
An amince kungiyar ta Stamford Bridge ta kashe fam 500,000 a wasannin gida, ta kuma kashe fan 20,000 a wasannin waje.
A kalla ana kashe fam 30,000 wajen gudanar da gasar Premier League da kuma wasannin waje a gasar Zakarun Turai da wasu karin tsarabe-tsarabe.



























