Europa League: Barcelona ta kai zagayen quarter a gasar Zakarun Turai

Asalin hoton, Barcelona FC
An wallafa
Barcelona ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa League, bayan da ta doke Galatasaray 2-1 a Istambul ranar Alhamis.
Galatasaray ta fara cin kwallo ta hannun Marcao a minti na 28 da fara tamaula, daga baya Barcelona ta farke ta hannun Pedro Gonzalez Lopez.
Bayan da suka koma zagaye na biyu a minti na hudu, Pierre-Emerick Aubameyang ya ci wa Barcelona kwallo na biyu kuma na bakwai a wasa 10 da ya yi wa kungiyar ta Camp Nou..
Ranar 10 ga watan Maris kungiyoyin sun tashi 0-0 a wasan farko a Camp Nou, kenan Barcelona ta kai zagaye na biyu da kwallo 2-1 gida da waje.
Ranar Juma'a za a raba kungiyoyi takwas da suka rage domin buga quarter finals a gasar ta Europa League.























