Lionel Messi ya kara cin karo da koma baya a Paris St Germain

Asalin hoton, Getty Images
Paris St Germain za ta ziyarci Monaco domin buga wasan mako na 29 a gasar Liguea da za su kara ranar Lahadi.
To sai dai kuma kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi ba zai buga wasan ba, sakamakon rashin lafiya, wanda bai yi atisaye ranar Juma'a ba.
Saboda da Messi Messi zai koma buga wa PSG tamaula, bayan ya dawo daga Argentina wadda za ta kara a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.
Argentina za ta karbi bakuncin Venezuela a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Tuni Argentina ta samu gurbin buga gasar da za a yi cikin Nuwamba da Disambar shekarar nan da makinta 35, bayan da Brazil ke jan ragama mai maki 39.
Messi ya buga wa PSG wasa 18 daga 28 da ta kara a Ligue 1 a bana, wanda ya ci kwallo biyu, amma shine kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga mai 11.
PSG ta ci karo da koma baya a kakar bana, bayan da Real Madrid ta yi waje da ita a wasan zagaye na biyu a Champions League.
Haka shima Sergio Ramos wanda ya buga wa PSG karawa biyar na murmurewa daga jiny da ya yi, amma ba zai buga fafatawa da Monaco ba.



























