Na shiga damuwa lokacin Mourinho yana United - Pogba

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya ce ya shiga damuwa, bayan da ya samu rashin jituwa da Jose Mourinho a lokacin da yake koci a Old Trafford.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin dan wasan, mai shekara 29 da Mourinho, wanda ya karbe mukamin mataimakin kyaftin dafa wajen Pogba.
To sai dai kuma a cikin watan Disambar 2018, United ta kori Mourinho.
''Na shiga hali na damuwa karo da dama a sana;ar tamaula da nake yi, sai dai ba za ka tattauna kan batun ba.
''Wasu lokacin, ba za ka san kana cikin damuwa ba, kawai za kaji ba ka son shiga mutane, kuma ba ka son yin magana da kowa.
''Ni kaina na fara shiga wannan yanayin a lokacin da Mourinho ke kocin Manchester Unted. Sai ka tambayi kanka kaine kakae da laifi, saboda ba ka taba samun kanka cikin wannan yanayin ba a rayuwa.''
Pogba ya koma United da taka leda kan fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya a 2016, a kuma lokacin Mourinho ya maye gurbin Louis van Gaal a kakar gaba.
Mourinho ya lashe League Cup da Europa League a 2017 tare da United, daga baya dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da 'yan wasu 'yan wasa da mahukuntan kungiyar.



























