Virgil van Dijk na fatan lashe kofuna a bana a Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata Liverpool za ta ziyarci Benfica, domin buga wasan farko a zagayen Quarter finals a Champions League.
Virgil van Dijk ya ce Liverpool ba za ta yi sakaci a karawar da za ta yi da kungiyar Benfica ba, a shirin da take na lashe kofuna da yawa a kakar nan ba.
Liverpool wadda ke fatan daukar kofi hudu a bana ta dauki Caraboa, sannan maki daya ne tsakaninta da Manchester City, wadda take ta daya a teburin Premier League, sannan ta kai daf da karshe a FA Cup a bana.
''Muna son kakar nan ta zama wadda ba za mu munta da ita ba, wajen samun nasarori,'' in ji Van Dijk.
''Za mu ci gaba da sa kwazo'' a wasanninmu - bayan da sauran kungiyoyi ke kara sa kaimi.
''Ba wanda zai dauka cewar za mu kawo wannan matakan tare da dukkan 'yan wasanmu''.
Mai tsaron bayan Liverpool, wanda ya sa hannu kan kaka uku a Anfield a bana, ya yi wasa biyar a bara, bayan da ya ji rauni cikin watan Oktoban 2020.
Tun kan raunin, an yi hasashen cewar Van Dijk daya ne daga fitattun masu tsaron baya a duniya, wanda ya taka rawar gani a Liverpool da ta kai ta lashe Premier League a 2019-20 da kuma Champions League.
Liverpool za ta buga karawar da dukkan 'yan wasanta, bayan da Naby Keita da Trent Alexander-Arnold, sun yi zaman benci a gasar Premier League da kungiyar Anfield ta ci Watford ranar Asabar.



























