'Yan Barcelona da za su kara da Frankfurt a Europa League

Asalin hoton, Barcelona FC
Eintracht Frankfurt ta karbi bakuncin Barcelona, domin buga wasan quarter finals a Europa League da za su fafata ranar Alhamis.
Barcelona za ta buga karawar, bayan da ta koma ta biyu a teburin La Liga, sakamakon cin Sevilla 1-0 ranar Lahadi a babbar gasar tamaula ra Sifaniya.
Tuni kociyan Barcelona, Xavi Hernández ya bayyana 'yan wasa 21 da ya je da su Jamus tun ranar Laraba, domin buga karawar.
Za kuma su buga wasan farko a zagayen Quarter finals, yayin da ake sa ran buga wasa na biyu a makon gobe a Camp Nou.
'Yan wasan Barcelona: Ter Stegen, Piqué, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Adama, Braithwaite, Neto, Lenglet, Pedri, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Nico, Gavi, Balde da kuma Arnau Tenas.
Memphis ba zai buga karawar ba
Dan wasan Barcelona, Memphis Depay ba zai buga karawar ba yana jinya, sauran da ba za su buga wasan ba da ke jinya sun hada da Sergiño Dest, Sergi Roberto, Ansu Fati da kuma Umtiti.
Luuk de Jong shima ba zai yi wasan ba, sakamakon ya kamu da cutar korona, shi kuwa Dani Alves ba zai yi wasan ba, bayan da Barca ba ta yi masa rijistar buga gasar ba..



























