Paris St Germain za ta yi wa Kyalian Mbappe tayin fam miliyan 150 a kaka biyu

Kylian Mbappe celebrates scoring against Real Madrid
An wallafa

Paris St-Germain na shirin gabatar da kunshin kwantiragin fam miliyan 150 ga Kylian Mbappe, domin ya ci gaba da zama a kungiyar kaka biyu nan gaba.

Wannan labarin ya fito ne daga wajen kwararre a fagen sharhin tamaula dan kasar Sifaniya, Guillem Balague.

Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 23 za ta kare a PSG a karshen kakar nan, wanda ya amince da farashin da Real Madrid ta taya shi a watan jiya.

Sai dai kuma PSG na bin duk hanyar da ta dace, domin ganin dan kwallon ya ci gaba da taka leda a kungiyar, har ma ta ce za ta ke biyansa albashin fam miliyan 21 a kowacce shekara.

Duk da wannan tayi mai tsoka da PSG ke yi wa dan kwallon, hankalinsa ya karkata ga Real Madrid.

Da yake ganawa da 'yan jarida bayan da ya ci Lorient kwallo biyu, Mbappe ya ce ''Tuni na yanke shawara, akwai abubuwan da na yi la'akari da su. Wannan abun sabo ne.''

PSG na ci gaba da rarrashin Mbappe dan kwallon tawagar Faransa da ya saka hannu kan tsaiwaita zamansa har zuwa bayan gasar kofin duniya da za a yi a Qatar tsakanin Nuwamba da Disamba.

Tun farko kungiyar da ke Faransa ta gabatar masa da kunshin yarjejeniyar fam miliyan 125, yanzu kuma ta yi niyar kara fam miliyan 25 a kai.

Real Madrid ta zura ido kan lamarin, bayan da ta kwan da sanin cewar ta cimma yarjejeniya da dan kwallon, shi ya sa ta bar neman Erling Haaland, bayan da Mbappe ya amince zai koma Santiago Bernabeu.