Levante vs Barcelona: 'Yan kwallon Barcelona da suka je Levante buga La Liga

Barcelona FC
An wallafa

Barcelona ta ziyarci Levante, domin buga wasan mako na 31 a gasar La Liga da za su kece raini ranar Lahadi a filin wasa na Ciutat de Valencia.

Ranar 26 ga watan Satumbar 2021, kungiyoyin sun fafata a Camp Nou, inda Barcelona ta yi nasara da ci 3-0.

Wadanda suka ci mata kwallayen a fafatawar sun hada da Memphis Depay da Luuk de Jong da kuma Ansu Fati.

Barcelona mai kwantan wasa tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 57, ita kuwa Levante mai maki 22 tana ta 19 a kasan teburi.

Real Madrid ce ke jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana da maki 72, sai Sevilla ta biyu mai maki 60.

Tuni kociyan Barcelona, Xavi Hernandez ya bayyana 'yan wasa 21 da za su buga masa fafatawar.

'Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Adama, Braithwaite, Neto, Nico, Lenglet, Pedri, L. De Jong, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Carevic da kuma Gavi.

Wadanda ke jinya:

Dest, Piqué, Memphis, Ansu Fati, S. Roberto da kuma Umtiti.