Real Madrid vs Chelsea: Lukaku ba zai je Real Madrid ba ranar Talata

Chelsea boss Thomas Tuchel
An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu na daf da na kusa da na karshe a Champions League ranar Talata.

A wasan farko da suka buga ranar Laraba 6 ga watan Afirilu, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Stamford Bridge.

Karim Benzema ne ya ci Chelsea kwallaye ukun rigis, ita kuwa kungiyar Stamford Bridge ta zare daya ta hannun Kai Havertz.

To sai dai kuma Chelsea za ta ziyarci Sifaniya ba tare da Romelu Lukaku ba, wanda ya buga karawar farko a Ingila amma yana jinya.

Dan kwallon tawagar Belgium bai yi wa Chelsea wasan Premier League ba ranar Asabar da ta caskara Southampton 6-0 a St Mary.

Sai dai kyaftin, Cesar Azpilicueta ya bi Chelsea zuwa Real Madrid, wanda bai buga wasan Premier League ranar Asabar ba, sakamakon jinyar cutar korona.

Shi kuwa dan wasa, Ross Barkley bai da lafiya - haka kuma Callum Hudson-Odoi da Ben Chilwell har yanzu ba su warke ba.

Duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci Manchester City ko kuma Atletico Madrid a karawar daf da karshe.

City ce ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya da ci 1-0 a wasan farko a quarter finals da suka fafata a Etihad.

A bara Chelsea mai rike da Champions League ce ta fitar da Real Madrid, kafin daga baya ta doke City ta lashe kofin Zakarun Turai.

Ko a bara sai da Napoli ta doke Chelsea 3-1 a zagaye na biyu a gasar ta Zakarun Turai, sai ta kai zagayen gaba da ci 5-4 gida da waje.