Bayern Munich vs Villareal: Wasu batutuwa da ya kamat ku sani kan fafatawar

Bayern Villareal
An wallafa

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Villareal a wasa na biyu a quarter finals a Champions League da za su fafata ranar Talata.

A wasan farko da suka kece raini a Sifaniya, Villareal ce ta yi nassara da ci 1-0, kuma Arnaut Danjuma ya ci mata kwallon a minti na tara da fara wasan.

To sai dai kuma da wasu batutawa biyar da ya kamat ku sani kafin wasan da za su fafata ranar Talata.

1. Bayern za ta iya cin wasa na 159 a Champions League

Idan har Bayern Munich ta doke Villarael a wasan da za su kara ranar Talata, nasara ta 159 kenan a Champions League, za kuma ta hau kan Barcelona, amma ta biyu bayan Real Madrid da ke kan gaba mai nasara 172 a tarihi.

2. Bayern ta sha kai wa zagayen gaba, bayan an doke ta a wasan farko

Sau uku ana cin Bayern Munich a wasan farko a waje, amma ta kai zagayen gaba idan an zo gidanta - shine wanda ta doke Porto a 2014/15 a zangon quarter finals da wanda ta yi wa Basel a 2011/12 a zagaye na biyu da wanda ta yi nasara a kan Real Madrid a 2006/07 a zagayen kungiyoyi 16.

A gasar Europa Cup kuwa, sau hudu kungiyar Jamus kan kai wasan gaba, bayan da aka doke ta a karawar farko da ta yi a waje.

3, Bayern tana da karfi a gida a Champions League

Bayern ta yi nasara a wasa 12 daga 13 da ta kece raini a baya a gasar ta Zakarun Turai, in banda wanda Paris St German ta doke ta 3-2 a Quarter finals a kakar bara.

A kakar nan kuwa kungiyar Jamus ta ci dukkan wasa hudun da ta yi a Allianz Arena, kuma da kwallaye uku kan ci.

4. Bayern ta dade rabon da ta kasa cin wasa a karawa biyu a jere

Sama da kaka uku kawo yanzu rabon da Bayern Munich ta kasa yin nasara a wasa biyu a jere - shine a kakar 2018/19, lokacin da ta yi canjaras biyu da rashin nasara a hannun Ajax da kuma sau biyu da Liverpool.

Rabon da a doke kungiyar Jamus karo biyu a jere tun Afirilun 2017 a quarter finals a hannun Real Madrid.

5. Lewandowski kan ci kwallaye da yawa a Allianz Arena

Robert Lewandowski kan ci kwallaye a Allianz Arena a gasar Champions League, wanda takwas daga 12 da ya ci a gasar bana a gida ya yi wannan bajintar a karawa hudu.