Sergio Ramos ya ce sai bayan kaka hudu ko biyar kan ya yi ritayar taka leda

Asalin hoton, Ramos/twirre
Sergio Ramos ya ce yana da shekara hudu ko biyar kafin ya yi ritaya daga taka leda - duk da kalubalen da yake fuskanta tun bayan da ya koma Paris St Germain.
Mai shekara 36 na fama da jinya a kakar farko da yake buga wa PSG tamaula, wanda ya yi minti 392 a wasa bakwai da ya yi kungiyar a duk fafatawa.
Tsohon dan kwallon Real Madrid, mai tsaron baya ya taka rawar gani a karawar da PSG ta casa Clemount 6-1, wasan da Neymar da kuma Kylian Mbappe kowanne ya ci uku-uku rigis.
Sai dai kuma Ramos bai ce komai ba kan buga wa tawagar Sifaniya tamaula, bayan da ya yi mata tamaula 180 da lashe kofin duniya da kofin Nahiyar Turai biyu.
Kusan dai yanzu ya yi ritaya daga buga wa Sifaniya kwwallo, bayan da Luis Enrique bai gayyace shi gasar nahiyar Turai ta 2020 ba, kuma bai nuna yana son komawa buga mata wasanni ba, wadda za ta buga gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
PSG tana kan gaba a teburin babbar gasar tamaula ta Faransa ta bana da tazarar maki 12 tsakaninta da Marseille ta biyu a Ligue.























