Bayren Munich 1 - 1 Villareal: Dan Najeriya ya fitar da Bayern daga Champions League

Samuel Chukwueze
Bayanan hoto, Kwalo biyu Chukwueze ya ci wa Villarreal a Champions League
An wallafa

Villareal ta kai karawar daf da karshe a Champions League, duk da tashi 1-1 da ta yi a gidan Bayern Munich ranar Talata.

A ranar Laraba 6 ga watan Afirilu Villareal ta ci Bayern Munich 1-0 a wasan farko da suka kara a Sifaniya a zagayen daf da na kusa da na karshe.

Robert Lewandowski ne ya fara ci wa Bayern kwallo, bayan da suka koma daga hutun rabin lokacin a Allianz Arena.

Sauran minti biyu a tashi daga wasan Samuel Chukwueze ya farke kwallon da ya kai kungiyar Sifaniya zagaye na daf da karshe a Champions League.

Da wannan sakamakon Villareal za ta fuskanci duk wadda ta yi nasara tsakanin Liverpool da Benfica da za su kece raini ranar Laraba.

Ranar Talata 5 ga watan Afirilu, Liverpool ta doke Benfica 3-1 a wasan farko zagayen kwata fainal a Portugal.

Unai Emery na fatan lashe Champions League a karin farko, bayan da ya dauki Europa League biyu a Sevilla da daya a Villareal a bara.