Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Kane, Ronaldo, Bergwijn, Rudiger, Carlos, Botman

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Ingila Harry Kane na shirin watsi da tayin da ya samu daga Manchester United a wannan kakar domin ci gaba da zama a Tottenham, yayin da ita kuma Man Utd ke shirin sanar da sabon kocinta Erik Ten Hag. (Mirror)
Ten Hag, ɗan ƙasar Netherlands, ya shaida wa manyan Manchester United cewa ba zai daidaita da salon taka ledar ɗan wasan gabanta Cristiano Ronaldo, mai shekara 37 ba. (Star)
Ten Hag na duba yiwuwar dauko ɗan wasan gefe a Tottenham Steven Bergwijn, mai shekara 24, idan ya soma horas da United.(Mail)
Sannan United ta kara yawan kudin tayi kan ɗan wasan da suke fafata sayen shi tare da Barcelona Antonio Rudigerbid na Chelsea.(Sun)
Ɗan wasanNorwich Max Aarons ya kasance mutumin da United da Arsenal ke hari, yayinda Bayern Munich da Borussia Dortmund su ma ke nuna zawarcinsu a ɓoye. (Sun)
Ɗan wasanSevilla Diego Carlos, mai shekara 29, na iya kasance zaɓin Newcastle United a wannan kakar, idan ta gaggara daidaitawa da Sven Botman, da ke nazarin barin Lille zuwa AC Milan. (Chronicle)
Manchester City na farautar ɗan wasan Monaco Aurelien Tchouameni, yanzu haka ta sanya shi cikin jeren manyan 'yan wasa da take son sayo wa domin maye gurbin Fernandinho. (Football Insider)
Borussia Dortmund ta yi nasara a farautar ɗan wasan Red Bull SalzburgKarim Adeyemi, wanda aka rinka alakantawa da Liverpool. (Sky Germany - in German)
Tottenham ta sake nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Inter MilanLautaro Martinez a wannan kakar wanda tun watan Janairu take gwada sa'arta, sai dai za ta fuskanci kalubale daga wajen Atletico Madrid.(Football Transfers)
Villarreal za ta tattauna da Tottenham kan Giovani lo Celso wanda ya tafi zaman aro tun watan Janairu. (Football Insider)
Leeds United ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan Croatia, Josko Gvardiol, wanda ta kusan saye shi lokacin da ya baro Dinamo Zagreb saboda RB Leipzig a 2020. (Football Insider)
Manchester City ta zura ido don ganin yadda za ta kaya a tayin da ta gabatar kan ɗan wasan Algeria Riyad Mahrez, da ɗan wasan Ingila Raheem Sterling, da na Brazil Gabriel Jesus. (Teamtalk)
Brentford ta tuntubi Shakhtar Donetsk kan ɗan wasan Ukraine din nan mai shekara 21 Mykhaylo Mudryk. (90min)



























