Porto ta amince ta sayar wa Arsenal dan wasanta Fabio Vieira a kan £34m

Asalin hoton, Getty Images
Porto ta ce sun amince su sayar da dan wasan tsakiya Fabio Vieira ga Arsenal a kan euro 40m (£34.2m).
Kungiyar ta kasar Portugal ta fitar da sanarwar da ke cewa Arsenal za ta soma biyan euro 35m (£29.9m) domin daukar Vieira ko da yake za a kara 'yan tsarabe-tsarabe.
Har yanzu dan wasan, mai 22, bai lashe wani babban kofi ba a Portugal sai dai an zabe shi a matsayin gwarzon dan kwallon Turai na kakar wasan da ta wuce a rukunin 'yan kasa da shekara 21.
Ya taimaka sau 14 wajen zura kwallo a Primeira Liga a kakar wasan bara.
Kazalika Vieira ya ci kwallo shida a wasan lig 27 da ya buga a yayin da ya taimaka wa Porto ta sake daukar babban kofin lig na Portugal.
Ya buga wa Portugal wasa 21 na 'yan kasa da shekara 21 kuma zai kasance dan wasa na uku da Arsenal za ta dauka a bazara, bayan golan Amurka Matt Turner da matashin dan wasan gaban Brazil Marquinhos.























