Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Mun lalata jiragen yaƙin Amurka 81 - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 8 ga watan Oktoban 2026
Shin sulhun Sanata Barau da Abba Bichi zai ɗore?
Taron sulhun wanda ya gudana a Abuja a ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce shugabannin biyu sun samu damar tattauna saɓanin da ke tsakaninsu.
Ƴansiyasa 5 da suka yi wa Tinubu alƙwarin miliyoyin ƙuri'u a 2027
Daga arewacin ƙasar zuwa kudanci, an ji alƙawuran da suka kai miliyoyin ƙuri'u, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke cewa za su tabbatar da gagarumar nasara ga shugaban ƙasar.
Ƙasashen da Amurka ta yi amfani da sansanonin sojinsu a yaƙin Iran
Muhimmancin sansanin Fairford shi ne tun daga farkon yaƙin baya-bayan nan, ya zama sansanin da aka yi amfani da shi kai tsaye wajen ayyukan Amurka a cikin yankin Iran.
Yadda kogi ya tafi da yara uku ƴan gida ɗaya a Abuja
Wani mummunan ibtila'i ya auku a yankin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, inda wasu yara uku 'yan gida ɗaya suka rasa rayukansu bayan ruwa ya tafi da su a wani kogi.
Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP 25 a tafkin Chadi
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2026
Me zai faru idan kuna shan paracetamol fiye da kima?
A cewar Hukumar Lafiyar Birtaniya (NHS), mafi girman adadin paracetamol da babban mutum zai iya sha cikin sa'o'i 24 shi ne ƙwayoyi takwas na 500mg.
Abubuwa 10 da suka faru shekara uku bayan harin Hamas a Isra'ila
Ranar 7 ga Oktoba 2026 ce shekara uku tun lokacin da aka ƙaddamar da gagarumin harin a kudancin Isra'ila.
Yadda wani fasinja ya yi 'yunƙurin buɗe ƙofar jirgi' kafin saukarsa a Legas
Kamfanin jiragen sama na Kenya Airways ya tabbatar da mutuwar wani fasinja a cikin jirginsa da ke kan hanyarsa daga Nairobi zuwa Legas jim kaɗan kafin jirgin ya sauka a filin jirgin nama na Murtala Muhammed.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 8 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 8 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 8 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 8 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Premier League: Kociyoyi sun yi kalamai kan laifukan Man City
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 5 zuwa 10 ga watan Oktoban 2026.
United da Liverpool na son Truffert, Arsenal ta dage kan Alvarez
Manchester United da Liverpool na harin Adrien Truffert, Newcastle na son Tyler Morton yayin da Martin Odegaard na cikin jerin manyan ƴan wasan da ke shirin sabunta kwantaraginsu da Arsenal.
Yadda Messi ya yi bankwana da Argentina cikin hawaye
Tawagar Argentina ta yi bikin ban kwana da Lionel Messi, bayan ritaya daga buga mata wasanni, wanda ke kan gaba a ci mata kwallaye a tarihi.
'Abu uku da Messi zai yi bayan ritaya daga ƙwallon ƙafa'
Messi zai buga wa Argentina wasan karshe a wasan sada zumunci da Benin. BBC Sport ta duba menene abu na gaba ga ɗan wasan mai shekara 39?
Villa na sa ido kan Endrick, Bournemouth ba za ta siyar da Scott ba
Aston Villa na iya dauko Endrick zuwa gasar Firimiya, sai Bournemouth da ta shiga kokawar siyen Alex Scott, yayin da manya ƙungiyoyi ke son ɗaukar Rayan Cherki.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Mene ne ke ruruta wutar rikici a jam'iyyar APC a Kano?
"Wasu na yaɗa cewa duka maganganun da Sule Garo ya yi a Bichi da yawun gwamnan jihar ya yi tunda shi ya wakilta a taron".
Munanan haɗurran jiragen sama 14 da suka girgiza Najeriya
A tarihin sufurin jiragen sama a Najeriya, an samu hatsurruka masu yawa da suka shafi jiragen fasinja, jiragen soja da kuma jiragen haya.
Jagororin Taliban huɗu da Kotun ICC ta bayar da sammacin kama su
Cikakken bayanin sammacin ya kasance cikin sirri tun lokacin da aka bayar da shi, sai dai a ranar Litinin kotun ta bayyana sakamakon binciken alƙalan da suka amince da fitar da sammacin.
Mutum 12 sun jikkata bayan hari kan jirgi a mashigar Hormuz
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Talata 6 ga watan Oktoban 2026
Jihohin Najeriya 10 da suka fi yawan masu rajistar zaɓe a 2026
Bisa alƙaluman da hukumar ta fitar, wasu jihohi uku ne suka kasance a sahun gaba wajen yawan masu rajistar zaɓe, lamarin da ke nuna muhimmiyar rawar da za su taka a zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan da za a gudanar a shekarar 2027.
Yadda ƴan mata biyu tagwaye suka rasu a cikin sa'a 48 a Yobe
Wannan labari ya ɗauki hankalin jama'a ba kawai saboda rasuwar ƴan'uwan tagwaye cikin kwanaki biyu ba, har ma saboda kusancin da ke tsakaninsu da kuma matsayin iyayensu a fannin kiwon lafiya a Najeriya.
Jerin sunayen sojoji 25 da suka rasu a hatsarin jirgin soji a jihar Ondo
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hatsarin a matsayin "lokaci mai zafi" ga sojoji da kuma dukkan al'ummar kasar.
Jihohin Najeriya da jam'iyyun hamayya ke da ƙarfi gabanin zaɓen 2027
Duk da cewa APC ce ke mulki a matakin tarayya, akwai wasu jihohi da jam'iyyun hamayya irin su ADC da NDC da PDP da APM suka kafa tubali mai ƙarfi, lamarin da ya sa jihohin suka zama muhimman wuraren fafatawar siyasa.
Ni ne zan jagoranci gwamnatina, ba kamar Buhari ba - Peter Obi
Cikin hirarsa da BBC ɗantakarar shugaban ƙasara na jam'iyyar NDC ya bayyana yadda zai tunkari wasu matsalolin ƙasar huɗu idan aka zaɓe shi matsayin shugaban ƙasar a 2027
Ƙasashen Afirka 7 da aka fi biyan ma'aikata albashi mai gwaɓi
A cewar rahoton, matakan albashi suna bambanta ne saboda wasu dalilai daban-daban, ciki har da matakin ci gaban tattalin arziki da ƙwarewar ma'aikaci a aikinsa, datasirin wasu ɓangarori alal misali sassas da suka shafi na man fetur da ma'adinai da yawon buɗe ido da na ɓangaren kuɗi, da kuma buƙatun ƙungiyar ƙwadago. Sauran abubuwan da ke shafar kuɗin shigar ma'aikata sun haɗa da yawan haraji da hauhawar farashi da darajar kuɗin ƙasa da yanayin samar da ayyukan yi a kowace ƙasa.
Duka mutane 32 da ke cikin jirgin sojin Najeriya da ya faɗi sun mutu
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Litinin 5 ga watan Oktoban 2026
Ya dace ma'aikatan gwamnati su goyi bayan wani ɗantakara?
A lokuta da dama, ana samun muhawara game da ko ma'aikatan gwamnati na da damar nuna ra'ayinsu na siyasa a fili ko shiga yaƙin neman zaɓe ko kuma bayyana goyon baya ga wani ɗan takara ko jam'iyya yayin da suke kan mukamansu.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.