2017: Mura ta hana Sarauniya Elizabeth halartar addu'o'i

An wallafa

Fadar Buckingham ta sarauniyar Ingila, ta ce mura, ta sa Sarauniya Elizabeth, ba ta iya halartar addu'o'i da aka sabayi ba a duk lokacin da sabuwar shekara ta kama, a cocin dake rukunin gidajenta a Sandringham.

A cikin wata sanarwa, fadar ta ce shawarar da aka yanke ta rashin halartar Sarauniyar addu'o'in, wani mataki ne na taka-tsan-tsan.

Kafin Kirsimeti, Sarauniya Elizabeth, mai shekaru casa'in, ta yi fama da rashin koshin lafiya, kuma tun daga nan, ba a gan ta a bainar jama'a ba fiye da tsawon mako guda.

Sai dai fadar ta ce sarauniyar ta samu sauki a 'yan kwanakin nan.