Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da sauke faralli
Yayinda a gobe Lahadi ne ake sa ran hukumomin Saudi Arabia za su rufe filin jiragen sama na Jiddah ga jiragen mahajjatan bana, wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da zuwa kasa mai tsarki.
Maniyyatan da zuwa yammacin ranar Juma'a ba su samu tashi ba cikinsu ya duri ruwa domin suna ganin kamar za a hau arfar bana ba bu su.
Maniyyatan Jihar Neja ta arewacin Najeriya na cikin wadanda har yanzu ba su da tabbas a kan ko za su samu tashi.
Maniyyatan sun ce ana musu yawo da hankali, domin sai a kira su a kan cewa za su tashi, idan suka zo kuma sai a ce ba haka ba.
Kazalika sun kokawa da cewa har sun fara taba guzurinsu.
To sai dai kuma hukumar jin dadin alhazan jihar ta Neja ta musanta wannan zargin, inda ta ce ta na sa ne da halin da suke ciki kuma za a share masu hawaye.