Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Akwai illar amfani da maganin mallakar miji'
- Za ku iya latsa alamar lasifika da ke sama domin jin bayanin da ta yi.
Wata matar aure wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Fatima Zahra Umar a shirin Adikon Zamani cewa, "ba ta taba samun ikon mallakar mijinta ba sai lokacin da ta je wurin wata mai maganin mata na gyaran gida ta tsaga mata gabanta tare da sanya magani a ciki."
Ta ce "duk matan da suke cewa kayan mata ko kuma gyaran jiki karya ne to ba su san dawan garin ba ne kawai."
Irin wannan batu na gyaran jiki ko kuma tsare gida da mata ke yi na janyo kace-nace a tsakanin magidanta har ma da malaman addini.
To sai dai likitoci na cewa wannan dabi'a na da illa ga lafiyar matan da ma mazajensu.
Ku saurari abin da Dokta Hauwa Usman wata likitar mata a birnin Kano ta shaida wa Fatima Zahra Umar.
Karanta wadansu karin labarai