Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu cutar korona sun tsere daga cibiyar kula da su a Oyo
Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinde, ya ce biyu daga cikin mutum 33 da ke dauke da cutar korona sun tsere daga cibiyar kula da su.
Gwamnan ya bayana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba.
"Mun karbi karin sakamakon mutane 19 da ake jiran sakamakon gwajinsu na COVID-19. Sakamakon daya daga cikinsu ya nuna cewa ya kamu da cutar ranar 03/05/2020.Mutumin yana Ibadan.
"Sannan cikin mutanen da aka yi wa gwaji ranar 5 ga watan Mayu, mutum biyar sun kamu da ita," a cewar Gwamna Makinde.
Ya kara da cewa,"Daga cikin mutum 33 da ke dauke da cutar wadanda gwamnatin jiha ke kula da su, biyu sun tsere, watakila zuwa gidajensu. Yanzu hakan ya sa muna da masu dauke da cutar korona 31 a Oyo.