Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Burundi ta kori jami'an WHO saboda annobar coronavirus
Kasar Burundi ta kori wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a kasar tare da wasu kwararrun likitocin uku.
Wata wasika da ba a sanya hannu ba daga ma'aikatar harkokin waje ta bayyana wakilin naThere are no restrictions on movement in Burundi over the coronavirus pandemic WHO Dr Walter Kazadi Mulombo da wasu jami'ai uku a matsayin "wadanda kasar ba ta amince da su ba" kuma an basu su sa'o'i 48 su bar kasar.
Sauran su ne Farfesa Tarzy Daniel, Dr Ruhana Mirindi Bisimwa da Dr Jean Pierre Murunda.
Ministan Harkokin Wajen Burundi Ezechiel Nibigira bai musanta ko tabbatar da sakon da ke cikin wasikar ba, amma wata majiya a ma'aikatar ta tabbatar da sahihancinta ga BBC.
Ma'aikatar ba ta ba da dalilan korar jami'an ba.
Gwamnatin Burundi tana fuskantar suka game da shirya zabubbukan a yayin da ake fargaban barkewar annobar covid-19.
Ana gudanar da gangamin yakin neman zabe da 'yan takarar shugaban kasa ke gudanarwa a fadin kasar gabanin babban zabe na 20 ga Mayu, kuma ba a daukan matakan kariya da kamuwa da cutar - matakin da ke haifar da fargabar barkewar annoba a kasar.
Yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba, Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce gwamnatin Burundi tana rufa-rufa kan lamarin kuma wannan ya sa tana shakku kan ainihin adadin masu dauke da cutar korona da kasar ta sanar.
Kawo yanzu kasar ta ba da rahoton mutum 27 da suka kamu da cutar wadanda suka hada da mace daya.