Ɗan majalisar da ya shiga daji ya ceto ƴan mazaɓarsa da aka yi garkuwa da su a Kwara

An wallafa

Wani dan majalisar dokokin jihar Kwara Hon Sa'idu Baba Ahmad, kuma ɗan ƙungiyar sintiri ta ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, ya jagoranci wata tawagar ƴan sintirin da jami'an tsaro, wadda ta kuɓutar da wasu mutum 13 ƴan mazaɓarsa, da aka yi garkuwa da su.

Haka ma tawagar ta yi nasarar kashe ƴan bindiga huɗu a musayar wuta.

Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Gwanabe-Danmi- Adera ta yankin ƙaramar hukumar Kaiama ya shaida wa BBC cewa sai da suka kwashe kwanaki suna sintiri a cikin dajin da ake kira Old Oyo National Park kafin su cimma 'yan bindigar.

Ya ce sun kwana uku suna shiga daji suna farautarsu inda daga bisani suka samu nasarar kuɓutar da mutum 13 da suka yi awon gaba da su.

Hon Sa'idu ya kuma ƙara da cewa babu mutum ko guda da ya ji ciwo a cikin waɗanda suka ceto ɗin, dukkansu suna da ƙoshin lafiya, kana wadanda suka nuna alamar galabaita sun kai su asibiti ana duba su.

''Mun samu gawawwaki hudu a cikin 'yan bindigar, kana mun ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 da kwanson harsasai shida da harsasai guda 67,'' in ji shi.

Ya ci gaba da cewa sai dai ba su samu sun kama sauran 'yan bindigar ba wanda adadinsu su tara ne, guda biyu dai sun tsere da raunukan harsasai.

Haɗin gwiwa

Wannan gagarumar nasarar dai in ji dan majalisar sun same ta ne ta hanyar gangamin haɗin gwiwa da 'yan sintiri na Fulani da na Yarbawa, tare da sojoji da ƴan sanda har da shugaban ƙaramar hukumar ta Kayama.

''Sai da muka kasu gida biyu da tawagarmu da ta jami'an tsaro, amma tawagarmu ce ta yi arangama da su.

''Muhimmancin wannan sintirin da muka yi shi ne muddin muka bari suka yi kaka gida a wajen za su hana mutanenmu walwala, amma Alhamdlillahi da muka tarwatsa su yanzu za a samu zaman lafiya,'' in ji shi.

Dan majlisa Sa'idu Baba Ahmed ya bayyana cewa dama tun kafin ya zama ɗan majalisa yana ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a jihar ta Kwara.

Ya kuma riƙe muƙamin sakataren ƙungiyar har na tsawon shekara takwas yana kuma gudanar da ayyukan sintiri a cikin kungiyar.

Yanzu haka dai in ji dan majalisar sun mika gawawwakin 'yan bindigar hudu da suka rasa rayukansu a musayar wuta da bindigogi da harsasan ga rundunar ƴan sandan Najeriya.