Dubai Open: An doke Murray, Nadal, Djokovic da Medvedev sun tsallake

Andy Murray
An wallafa

An sake fitar da Andy Murray a zagaye na biyu a gasar Dubai Open, bayan da Jannik Sinner dan kasar Italiya ya lallasa shi 7-5 6-2.

Murray wanda dan Burtaniya ne na harin cin wasa na 700 a tarihi amma kuma hakan ba ta samu ba.

Wannan ne karo na hudu ana cire shi a zagaye na biyu a bana, kama daga gasar Australian Open da aka yi a watan Janairu.

Daga nan kuma aka fitar da shi zagaye na biyu a Rotterdam da Qatar yanzu kuma ga Dubai Open.

To sai dai yayin da aka fitar da Andy Murray, dan wasan duniya Novak Djokovic da na uku Daniil Medvedev sun kai bantensu a zagayen gaba na Dubai Open din.

Murray

Medvedev ne ya buga wasan karshe a Melbourne da Rafael Nadal a Australian Open amma bai yi nasara ba.

Shi kuwa Djokovic da ya tafi Melbourne rike da kofin gasar ta Australian open bai samu damar kare kambunsa ba, a dalilin soke masa takardun bisa kan cewa ba a yi masa rigakafin korona ba kafin ya shiga kasar.

A yanzu Novak Djokovic na fuskantar barazanar saukowa daga na daya, matsawar Medvedev da ke na uku ya fishi taka rawa a gasar Dubai da ta Acapulco.