Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan majalisar Amurka zai iya rasa kujerarsa saboda ɗan Najeriya
Wani dan majalisar dokokin Amurka na jam'iyyar Republican na fuskantar hadarin korarsa daga majalisar, saboda karya da ya yi kan wani tallafin kudi na siyasa da ke da alaka da wani attajiri dan Najeriya.
Masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya sun gano cewa Jeff Fortenberry, dan majalisar wakilai daga Nebraska, ya yi wa jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, karya kan karbar tallafin da ya saba wa doka, daga attajiri Gilbert Chagoury, wani hamshakin attajirin dan kasuwa dan Najeriya.
Yanzu dai a sakamakon wannan bincike da masu taimaka wa alkalin suka yi inda suka gano cewa dan majalisa Jeff Fortenberry ya shirga wa jami'an na FBI, masu binciken laifuka karya game da kudin tallafin na siyasa da attajirin dan Najeriya ya ba shi, zai iya rasa kujerarsa ta wakilci a majalisar.
Sannan kuma bayan rasa kujerar, zai iya fuskantar daurin shekara 15 a gidan maza, a bisa laifuka uku.
Batun dai ya kara jan hankali a kan irin tasirin da 'yan kasashen waje ke yi a siyasar Amurka.
A bisa dokar Amurka, haramun ne ga 'yan kasashen waje su bayar da wani tallafi na siyasa, to amma kuma Mista Chagoury, mai shekara 75, ya dade yana yin hakan.
A shekara ta 2019, gwamnatin Amurka ta ci tararsa dala miliyan 1.8, kuma aka gudanar da bincike a kan wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar tallafin nasa.
A shekara ta 2016, ne ya bayar da tallafin da ya saba doka na dala dubu 30 ga dan majalisa Fortenberry, amma ta hannun wasu masu bayar da tallafi a yayin wani taro a Los Angeles.
Mista Chagoury, dan kasuwa da ke zaune a Paris ya yi fice sosai, domin har sunansa an rubuta a wani bangare na gidan adana kayan tarihi na Louvre da ke Paris wanda shi ne gidan adana tarihi da aka fi ziyarta a duniya.
A wani lokaci kuma an taba hana shi takardar izinin shiga Amurka bisa zarginsa da alaka da mayakan kungiyar Hezbollah.
Haka kuma ya taba kasancewa babban mai bayar da shawara ga tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, marigayi Janar sani Abacha, a shekarun 1990.
Bugu da kari Mista Chagoury ya kasance jakadan kasar St Lucia, wadda tsibiri ce, a Vatican.
Shi da dan majalisa Fortenberry, mai shekara 61, sun kasance masu bin darikar Katolika sau da kafa, kuma ana danganta su da wata kungiyar agaji ta Kirista da ke birnin Washington, mai suna In Defense of Christians.
Zuwa yanzu jami'ai ba su bayar da cikakken bayani ba a kan dalilin da ya ware wannan dan majalisa ya ba shi tallafin, sai dai takardun sheda na Ma'aikatar Shari'a ta Amurka sun nuna cewa an ba Mista Chagoury shawara ne kan ya bayar da shi ga 'yan siyasar Amurka da suka fito daga wata jiha da ba ta yi fice ba, maras yawan jama'a domin a nan ne za a fi ganin tallafin.
A wata hira ta waya da aka nada ta sirri, an gaya wa Fortenberry cewa ana ganin ya karbi kudi har dala dubu 30, ba bisa ka'ida ba ta hannun abokan huldar Mista Chagoury.
To amma kuma a lokacin ganawarsa da jami'an hukumar bincike ta FBI, Fortenberry ya musanta karbar wannan kudi, ya ma nuna ba shi da wata masaniya a kai, bugu da kari ya ce, magana ce ma da za a ce ta tayar masa da hankali.
Masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa daga nan ne ya yi ta kokarin boye tallafin domin ya kare aikinsa da kimarsa da kuma aminansa na kurkusa.
A ranar Alhamis ne masu taimaka wa alkalii yanke hukunci a Los Angeles suka tattauna kan shari'ar tasa tsawon kusan sa'a biyu, kafin daga karshe su same shi da laifin yin karya da kuma boye gaskiya ga masu bincike na tarayya.
Babban mai gabatar da kara Mack Jenkins ya ce, tarbiyya daga gida take farawa, ''idan muna son wani ya bi doka, to hakan zai fara ne daga masu yin doka, wato 'yan majalisa, domin mun dauke su da kima sosai.''
Ana sa ran yanke masa hukunci a ranar 28 ga watan Yuni, amma kuma ya ce zai dukaka kara.
Kodayake babu bukatar ya sauka daga kujerarsa, amma 'yan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Republican da kuma na Democrat sun bukace shi da ya yi murabus.
Idan kuma ya ki, to kusan ba shakka za a kore shi daga majalisar, kamar yadda a baya aka yi wa wasu 'yan majalisar da aka samu da laifuka.