Arsenal na son Bynoe-Gittens, City ta kwadayin Kimmich, Sancho zai tashi daga United

.
An wallafa

Arsenal ce ke kan gaba wajen neman dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 19 da Ingila Jamie Bynoe-Gittens. (Bild Germany)

Manchester City ta matsu ta kara wa dan wasan gabanta na Norway Erling Haaland, mai shekara 23, sabon kwantiragi don hana Real Madrid da Barcelona dauakrsa. Haaland ya ci kwallaye 44 a wasanni 43 na gasar Premier. (Gazzetta dello Sport)

Wani mamba a hukumar kwallon kafa ta Real Madrid ya ce yana fatan dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe zai zabi komawa kungiyar ta Spaniya idan kwantiragin dan wasan mai shekaru 24 da Paris St-Germain ya kare a bazara mai zuwa. (AS Spanish)

Manchester United ta saka dan wasan baya na Sporting Lisbon da Portugal Goncalo Inacio, mai shekara 22, cikin jerin ‘yan wasan da suke zawarcinsu, yayin da take kokarin karfafa bayanta a bazara mai zuwa. (Mirror)

Ana sa ran dan wasan tsakiyar Manchester City Kalvin Phillips zai bar kungiyar a watan Janairu, inda Newcastle United da Everton ke cikin wadanda ke zawarcin dan wasan na Ingila mai shekaru 27. (The I)

Arsenal na kokarin daukar dan wasan gaba na kasar Ingila Ivan Toney daga Brentford kuma tattaunawa ta gudana tsakanin kungiyoyin biyu, yayin da ita ma Chelsea ke zawarcin dan wasan mai shekaru 27. (Talk)

Jamaica za ta iya ba wa dan wasan gaban Manchester United Mason Greenwood mai shekara 22, wanda ke taka leda a Getafe ta Spaniya, damar wakiltarta a a gasar kwallon kafa ta kasa da kasa shekaru uku bayan ya wakilci Ingila. (Mirror)

Manchester City na zawarcin dan wasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich kuma Bayern Munich ta ce za ta iya siyar da dan wasan mai shekaru 28 idan bai tsawaita kwantiraginsa ya wuce shekara ta 2025 ba. (90 Min)

Dan wasan Manchester United da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 23, a shirye yake ya koma wata kunigiyar a a watan Janairu, kuma Juventus da Borussia Dortmund, wato tsohon kulob dinsa na zawarcinsa. (The I)

Inter Milan ta yanke hukuncin sayen dan wasan gaba na Chelsea Armando Broja, mai shekara 22 a watan Janairu. (Fabrizio Romano)

Tsohon kocin Chelsea da Tottenham Antonio Conte a shirye yake ya karbi aikin kocin Napoli idan zakarun Seria A din suka sallami Rudi Garcia. (Calciomercato in Italia)

West Ham na shirin tattaunawa kan sabon kwantaragi da dan wasan baya na Faransa Kurt Zouma, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai kare a shekarar 2025. (Teamtalk)