Arsenal za ta ɗauko Kudus, Man Utd na nazari kan Zirkzee

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal a shirye take ta kashe fam miliyan 83 kan ɗanwasan tsakiya na West Ham Mohammed Kudus inda ɗanwasan ke son taka leda a Emirates domin samun damar buga wasannin Turai. (Fichajes - in Spanish)

Tottenham na shirin yin watsi da tayin Real Madrid kan ɗanwasanta mai shekara 26 na Argentina Cristian Romero. (Football Insider)

Manchester United na nazarin ɗauko ɗanwasan gaba na Netherlands Joshua Zirkzee a Janairu yayin da ƙungiyoyin Serie A ke sa ido kan ɗanwasan. (Calciomercato - in Italian)

Juventus na kan gaba a hamayyar ɗauko ɗanwasan gaba na Canada Jonathan David, mai shekara 24 daga Lille yayin da Manchester United da Liverpool da Inter Milan duka ke farautar ɗanwasan. (Footmercato - in French)

Manchester City na bibiyar golan AC Milan da Faransa Mike Maignan, mai shekara 29. (Fichajes - in Spanish)

Borussia Dortmund na nazarin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Sunderland da Ingila mai shekara 19 Jobe Bellingham. (Alan Nixon via Newcastle Chronicle)

Ɗanwasan baya na Bayern Munich da Canada Alphonso Davies na son sake aiki ƙarƙashin tsohon kocinsa Hansi Flick da ke Barcelona duk da Real Madrid da Manchester United na farautarsa. (Teamtalk)

Ɗanwasan tsakiyan na Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, na shirin kawo ƙarshen kwantaraginsa da Juventus domin komawa wata ƙungiyar idan har wa'adin haramcinsa ya cika. (Sky Sports)

Ɗanwasan gaba na Jamus Leroy Sane na shirin sanya hannu kan yarjejeniya da Bayern Munich amma ɗanwasan mai shekara 28 har yanzu bai kai ga amincewa da yarjejeniyar ba (Florian Plettenberg)

Tsohon ɗanwasan Spain Sergio Ramos, mai shekara 38, ba zai koma Real Madrid ba amma ƙungiyar za ta ɗauko ɗanwasan baya a Janairu, kuma ɗanwasan baya na Bayer Leverkusen ta Jamus Jonathan Tah, mai shekara 28 ne ƙungiyar ke mayar da hankali a kai. (Diario AS - in Spanish)

Masu farautar ƴanwasa na ci gaba da sa ido kan rawar da ɗanwasan tsakiya na Chelsea Kiano Dyer ke takawa yayin da kwangilarsa ke dab da kawo ƙarshe. (Mail)

David Moyes na son ya dawo gasar Premier yayin da Crystal Palace da Wolves da Southampton da Leicester suka nuna buƙatarsa. (Talksport)

Frank Lampard ne wanda ake ganin zai karɓi aikin horar da ƙungiyar Coventry City. (Sky Sports)