Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rabiot zai koma United daga Juve, Arsenal da Liverpool na gasa kan Yeremi Pino
Manchester United ta kulla yarjejeniya da Juventus kan sayen Adrien Rabiot, dan wasan tsakiya mai shekara 27 kan fam miliyan 15. (Guardian)
United ta kuma yi tuntuba kan dauko Guido Rodriguez, dan wasan tsakiya mai shekara 28 daga Real Betis. (AS - in Spanish)
Wani dan wasan gaba da United ke sha'awa shi ne Benjamin Sesko, dan kasar Slovenia, mai shekara 19, wanda kuma ake hasashen yana daf da amincewa da tayin komawa Red Bull Salzburg a 2023. (90min)
Chelsea na shirin yi wa Wesley Fofana tayi irinsa mafi tsoka a duniya da aka taba yi wa mai buga wasa a baya. Fofana mai shekara 21 na taka leda a Leicester City ne yanzu. (Football London)
Sai dai kungiyar ta Blues na da sauran aiki a gabanta, domin tayin da ta mika ya gaza wanda Leicester ke son gani da fam miliyan 10. (Independent)
Dan wasan gaba na Chelsea, Timo Werner mai shekara 26 zai koma RB Leipzig domin a duba lafiyarsa gabanin komawa tsohuwar kungiyar tasa. (Mail)
Roma ta yi watsi da tayin da Tottenham ta mika ma ta kan Nicolo Zaniolo, dan wasan gefe mai shekara 23 domin ya buga wasa a matsayin dan aron da za a iya sayewa baki daya daga baya. (90min)
Liverpool na fatan dauko Marcelo Brozovic, dan wasa tsakiya dan kasar Croatia mai shekara 29 daga Inter Milan domin ya karfafa 'yan wasan tsakiya na kungiyar. (Sport - in Spanish)
Arsenal da Liverpool duka sun bayyana sha'awarsu ta raba Yeremi Pino dan wasan tsakiya mai shekara 19 da Villareal. (AS - in Spanish)