Yadda mutanen gari suka yi kukan-kura suka kashe gomman ƴan bindiga a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
A wani al'amari da ya ɗauki hankali, mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara sun ce sun kashe aƙalla mutum daga cikin wani gungun ƴan bindiga bayan artabun da suka shafe kwana uku suna yi da su.
Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa mazauna ƙauyen sun ɗauki matakin tunkarar ƴan bindigar ne bayan sun gaji da hare-haren da ake kai musu akai-akai.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa sun fara shirin tunkarar ƴan bindigar ne bayan samun labarin cewa suna tafe zuwa ƙauyen.
Ya ce "Da suka zo, muka buɗe musu wuta, su ma suka riƙa harbe-harbe, mu kuma muna mayar da martani. Sun tafi da wasu daga cikin mutanenmu, amma mu ma mun kashe da dama daga cikinsu.
"Mun ga wasu daga cikinsu waɗanda ba ƴan Najeriya ba ne." in ji shi.
Mutumin ya ƙara da cewa sun gano gawarwakin mutum 18 ko 19 a wurin da aka yi artabun, yayin da ƴan bindigar suka tafi da wasu gawarwakin.
Ya ce ƴan bindigar sun yi goyon uku-uku ne a kan kowanne babur ɗaya, inda waɗanda suka kasa kwashewa suka bar a wurin.
Martanin Gwamnati
Mai ba wa gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan harkokin watsa labarai Jafaru Ƙaura ya tabbatarwa BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka tura ƙarin jami'an tsaro zuwa yankin domin ƙarfafa tsaro, da kare rayuka da dukiyoyin fararen hula, tare da hana 'yan bindigar sake dawowa domin kai wasu hare-hare.
Ya ƙara da cewa mutanen garin sun kashe sama da ƴanbindiga 30 yayin rikicin.
Ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya buƙaci mazauna ƙauyen na Birnin Tudu da sauran al'ummomin da ke kewaye da yankin da su ba jami'an tsaro haɗin kai, musamman ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko abin da suke zargi da ka iya kawo barazana ga tsaro.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, da jami'an tsaro da al'umma wajen gano waɗanda ke da hannu a ayyukan ta'addancin da kuma hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.
Me masana tsaro ke cewa kan hakan?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Captain Abdullahi Bakoji (mai ritaya) mutanen ƙauyen na Birnin Tudu sun yi abun a jinjina musu, duba da cewa kare kai yana daga cikin damarmakin da kundin tsarin mulkin Najeriya ba ba wa kowanne ɗan ƙasa.
A cewarsa ''Bai kamata a ce ko yaushe ana zuwa a kama ka kamar kaza ba., a je a daure ka a daji ana cukar da kai sannan a karbi kudade ba, shi kansa tsohon daraktan DSS ya taɓa jan hankaln mutane a kan hakan''
Sai dai Captain Bakoji ya yi gargaɗin cewa akwai buƙatar mazauna ƙauyen su ci gaba da kasancewa cikin shiri, yana mai cewa ƴan bindigar na iya komawa su sake shiri domin dawo wa da nufin ɗaukar fansa.
Ya shawarci mazauna yankin da su ƙarfafa tsarin tsaron al'umma, tare da tabbatar da cewa ana samun waɗanda za su riƙa gadin ƙauyen a kowane lokaci.
"Su ƙara shiri, su daina barci. Idan wasu sun yi barci, a samu wasu da za su tsaya su yi gadin gari. Sannan a sanar da jami'an tsaro, su ma su bayar da gudummawarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma," in ji shi.
Ba wannan ne karon farko ba
A wasu yankunan Najeriya da suka fuskanci matsalar tsaro, al'umma kan riƙa ɗaukar matakai daban-daban domin kare rayuka da dukiyoyinsu daga hare-haren ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
A wasu wurare kuma, mazauna yankunan kan haɗa kai wajen kafa ƙungiyoyin tsaron al'umma, waɗanda ke taimakawa wajen tattara bayanai da kai rahotannin abubuwan da ba su saba gani ba ga hukumomin tsaro.
Sai dai masana kan harkokin tsaro sun sha jaddada muhimmancin gudanar da irin waɗannan matakai bisa doka, tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro, domin kauce wa ɗaukar matakin da zai iya jefa rayukan fararen hula cikin haɗari ko haifar da ramuwar gayya.
Duk da cewa matakin da mazauna Birnin Tudu suka ɗauka ya nuna irin damuwar da al'umma ke ciki sakamakon hare-haren ƴan bindiga, tambayar da ke nan ita ce yadda za a tabbatar da cewa irin wannan artabu ba zai zama sanadin ƙarin zubar da jini ko kuma ramuwar gayya ba.
Masu sharhi kan harkokin tsaro na ganin cewa kare rayuka da dukiyoyin al'umma na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin mazauna yankuna da hukumomin tsaro, tare da samar da hanyoyin tattara bayanai da ɗaukar matakan gaggawa idan aka samu barazana.
Haka kuma masana na cewa akwai buƙatar hukumomi su ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan da hare-hare suka zama ruwan dare, domin jama'a su samu damar gudanar da harkokinsu ba tare da fargabar sace su ko rasa rayukansu ba.





























