Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rangers ta ɗauki Clement tsohon kociyan Monaco da Club Bruges
Rangers ta naɗa tsohon kociyan Monaco da Club Bruges, Philippe Clement a matsayin wanda zai ja ragamar kungiyar kan yarjejeniyar kaka uku da rabi.
Mai shekara 49, tsohon mai tsaron bayan tawagar Belgium ya maye gurbin Michael Beale, wanda aka kora a farkon watan nan.
Shi kanshi Clement an kore shi a watan Yuni a Monaco, bayan wata 18 yana horar da kungiyar da ta kare a mataki na shida a Ligue 1 a bara.
Cikin waɗanda suka nemi aikin horar da Rangers, mahukuntan ƙungiyar sun tattauna da Clement da kociyan Yokohama F Marinos, Kevin Muscat.
Shi dai Muscat tsohon wanda ya taka leda a Rangers ne mai tsaron baya, wanda yanzu yake aikin horar da tamaula.