Nigeria: An sace mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matarsa

An wallafa

Rahotanni a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sace wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda tare da matarsa a yayin da suke tafiya a mota.

An sace mataimakin kwamishinan nan ne a wani dajin da ke tsakanin Funtua a jihar Katsina da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wata majiya mai karfi ta tsaro a jihar Kaduna ta shaida wa BBC cewa, mataimakin kwamishinan na 'yan sandan na aiki ne a jihar Zamfara ko kuma a jihar Katsina.

Har yanzu dai rundunar 'yan sanda ta jihar ba ta ce komai ba kan wannan batu.

Amma kakin rundunar ya shaida wa wakilinmu Nura Muhammad Ringim cewa suna wani taro, inda ya bukace shi da ya sake kiransa bayan sun kammala.

Dajin da aka sace wannan mataimakin kwamishinan 'yan sanda dai dama sanannen wuri ne da aka yi amannar na kunshe da 'yan ta'adda kamar 'yan fashi da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Jihar Kaduna dai ta yi kaurin suna wurin sace-sacen mutane, inda ko a kwanakin baya sai da aka sace tsohon ministan kasar, Ambasada Bagudu Hirse.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro ke cewa suna daukar tsauraran matakai domin magance matsalar tsaro a jihar.