Barcelona ta kara nisa a saman teburi
An wallafa

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta bayar da tazarar maki 11 a saman teburi bayan 2-0 da ta ci Athletico Madrid a zazzafan wasan hamayya da suka buga a daren yau Asabar.
Luis Suarez da Lionel Messi ne suka ci wa Barce kwallaye masu kyan gaske, wanda ya kara dora su a hanyar lashe kofin La Liga na biyar cikin shekaru bakwai.
Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a kori tsohon dan wasan Chelsea Diago Costa bayan ya ci mutuncin alkalin wasa Jesus Gil a minti na 27.
Su kuwa Suarez da Messi ba su bari damar ta kubuce ba.
Suarez ne ya fara jefa kwallo ana saura minti biyar a tashi daga wasan, inda Messi ya ci kwallo ta biyu dakika 60 bayan haka a minti na 86.























