Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dattawan Igbo sun yi gargadi a kan 'kwararar almajirai zuwa kudu'
Kungiyar kare muradan al'ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta ja hankalin gwamnatin ƙasar a kan ta hanzarta ɗaukar mataki game da yadda ake samun wasu matasa da almajirai suna kwarara yankunan kudu daga arewacin ƙasar.
A baya-bayan nan dai ana ta yada bidiyon yadda ake kama matasa cikin tireloli a wasu jihohin kudancin Najeriya, da ake cewa sun fito ne daga arewa, ko da yake babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro da ta tabbatar da hakan.
Wannan na faruwa ne duk da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi da gwamnatin Najeriya da ma na wasu jihohin suka kafa da nufin hana yaduwar cutar korona.
Sai dai kungiyar ta ce ta gano cewa mutanen na ketawa ne ta dazuka domin shiga yankunan.
Dr John Nwodo, shi ne shugaban kungiyar na Najeriya, ya ce akwai damuwa game da yadda hukumomi suka yi shakulacin ɓangaro kan kiraye-kirayen da suke ta yi na dakile wannan matsala.
'' Mu a nan hankalinmu a tashe yake, an kama tare da tilastawa wasunsu komawa, akwai barazanar da Boko Haram ta yi a watan Janairu na kaddamar da yaki a kudu maso kudu''.
Ya ce ya yi magana da wasu abokansa jagorori a arewacin kasar amma har kawo yanzu babu wani mataki da suka dauka.
A cewarsa, ''Muna fargabar kada mutane su dauki matakin kare kansu idan har ta tabbata mutanen da ke kwarara yan bindiga ne, abin da kuma ba a fata.