Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Agboola Ajayi: Mataimakin gwamnan Ondo ya fice daga APC ya koma PDP
Mataimakin gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yamma a Najeriya Agboola Ajayi ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki ya kuma koma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan hana mataimakin gwamnan fita daga gidan gwamnatin jihar da ke Akure da kwamishinan 'yan sandan jihar Bolaji Salami da tawagarsa suka yi.
Ana tsammanin hakan ne babban dalilin da ya sanya Mista Ajayi ficewa daga jami'iyyar, yana mai cewa dalilin fitarsa a bayyane yake kowa ya sani.
Jim kadan bayan ficewar tasa Mista Ajayi ya bayyana komawarsa jam'iyyar adawa ta PDP tare da karbar katin shaidarsa na zama dan jam'iyya.
Mista Agboola Ajayi ya fita daga APC kwanaki kadan bayan gwamnan jihar Edo Godwin Obasaki ya fita daga jam'iyyar, saboda kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar a jihar Edo ya cire shi daga cikin waɗanda za su yi takarar, abin da ya yi sanadiyyar komawarsa jam'iyyar adawa ta PDP.
Kuma PDP ta tabbatar da cewa yana da damar shiga zaben fitar da gwani na jam'iyyar da za a yi ranar 25 ga watan Yuni.