Fashewar Beirut: Babu alamun akwai mutun raye a karkashin gine gine

An wallafa

Masu aikin ceto a babban birnin Lebanon wato Beirut sun fidda ran cewa za a iya samun mutanen da ake nema da rai, bayan fashewar sinadarai a tashar ruwan Beirut watan da ya gabata.

A ranar Alhamis ne na'urar ta nuna akwai alamun mutun a raye a cikin baraguzai, to amma bayan kwashe kashi 95 na baraguzan babu wani mutun da aka samu.

Yanzu haka akwai kusan masu aikin ceto hamsin a wurin, da suka hada da kwararru daga kasar Chile.

Fashewar sinadarin Ammonium nitrate a tashan ruwan ta Bierut ya yi sanadin mutuwar mutun 190, tare da jikkata dubbai.

A taron manema labarai shugaban tawagar masu aikin ceton Francisco Lermanta ya ce 'sun fidda ran cewa za a iya samun wasu a raye a karkashin ginin'.

Ya kara da cewa ko numfashin da aka ji kwanaki biyu da suka wuce na masu aikin ceto ne da ke aiki a wurin.

A yanzu hankali ya koma wurin gano gawawwakin wadanda har yanzu ba a gani ba, duk da Mr Lermanta ya ce suna fatan haduwa da abin mamaki.

Hukumomi a Lebanon sun ce har yanzu ba a gano mutun bakwai ba tun bayan fashewar.

A ranar Juma'a ne yan kasar suka yi shiru na tsawon minti daya, bayan cikar wata daya da fashewar ton 2,750 na sinadarin ammonium nitrate a tashar ruwan Beirut.