Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wilfred Ndidi: Aston Villa ta shirya biyan fam miliyan 50 ga dan wasan Najeriyar
Dan wasan tsakiyar Najeriya da Leicester City Wilfred Ndidi ya ce bashi da sha'awar barin Leicester City a yanzu, duk da shirin Aston Villa na mika tayin fam miliyan 50 kan shi.
Jaridar Daily Star ta Burtaniya ta ruwaito cewa Villa ta kammala shirye-shiryen taya Ndidi, kuma idan har ciniki ya fada a karshen kaka zai zama dan wasan mafi tsada da kungiyar ta taba saye a tarihi.
Ndidi ya buga wa Leicester wasanni 23 a bana, inda ya ci wa Foxes din kwallo daya.
To sai dai tsohon dan wasan Genk din ya ce '' ina jin dadin wasa da rayuwa a Leicester. Iyalina suna nan, ga shi ina karatun digiri kan kasuwanci.''
A bara Aston Villa ta sayi Emiliano Buendia daga Norwich City a kan fam miliyan 34, saboda haka idan kungiyar ta iya sayen Ndidi kan fam miliyan 50 zai zama dan wasa mafi tsada a tarihin kungiyar.
To amma mai horar da Leicester Brendan Rodgers ya ce dan wasan nasa ya haura abinda Villa ke son biya kansa.
" Dan wasa kamar Ndidi da ke da kwarewa da natsuwa ya haura haka. Ko wane koci zai so rike irinsa, amma dama na san sai ya ja hankalin kungiyoyi.'' In ji Rodgers.
Yanzu haka Ndidi na da sauran yarjejeniya da Leicester daga nan zuwa 2024.
Leicester City na fuskantar koma baya a bana, inda suka kasa cin wasa ko daya a cikin biyar, kuma suna zaune a na 11 a teburin Firimiyar Ingila.
Ta kuma kare na biyar kakar wasanni biyu da suka wuce.
Yau da daddare ne Wilfred Ndidi zai yi wa Leicester wasa na 200 a kofin Europa Conference League da za su buga da Randers FC a filin King Power.