Wasu ’yan Najeriya 105 sun sake komawa gida daga Afirka ta
Kudu, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa game da tsaron ’yan ƙasashen waje
gabanin wa’adin 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka ayyana.
’Yan Najeriyar sun isa Lagos cikin jirgin South African
Airways da misalin ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin
Wajen Najeriya ta bayyana.
Ma’aikatar ta shaida wa BBC yau Juma’a cewa gwamnati ta
taimaka wajen dawo da ’yan Najeriya 1,821 tun daga watan Yuni, sakamakon abin
da ta bayyana a matsayin sake ɓarkewar hare-hare kan baƙi da ’yan Afirka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Femi Adeniyi,
ya ce: “Ana ci gaba da ƙoƙarin kwashe ƙarin ’yan Najeriya da ke cikin mawuyacin
hali sakamakon fargabar tsaro a Afirka ta Kudu.”
Dawowar ta baya-bayan nan na zuwa ne ’yan kwanaki kafin 30
ga Satumba, ranar da wasu ƙungiyoyin masu adawa da baƙin haure suka ce ya
kamata ’yan ƙasashen waje da ba su da takardun zama su fice daga Afirka ta
Kudu.
An taɓa sanya makamancin wannan wa’adi a ranar 30 ga Yuni.
Dubban mutane sun shiga zanga-zangar adawa da baƙin haure a faɗin ƙasar, inda
aka bayar da rahoton aukuwar tashin hankali da sace-sace a wasu wurare. ’Yan sanda sun ce an kama kusan mutum 900,
galibinsu bisa laifukan da suka shafi shige da fice da sace-sace.
Hukumomin
Afirka ta Kudu sun jaddada cewa gwamnati ce ke da alhakin aiwatar da dokokin
shige da fice kuma sun gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu da kai
hare-hare kan ’yan ƙasashen waje.
Ba Najeriya kaɗai
ce ke taimaka wa ’yan ƙasarta ficewa daga Afirka ta Kudu ba.
Malawi ta ce ta
dawo da ’yan ƙasarta fiye da 38,000 tsakanin watan Yuni da farkon Yuli, yayin
da Zimbabwe ta ce sama da mutum 21,000 sun koma gida. Uganda, Ghana da
Mozambique ma sun dawo da wasu daga cikin ’yan ƙasarsu.
Hukumomin
Afirka ta Kudu sun ce zuwa ranar 11 ga Yuli, an kammala shirye-shiryen mayar da
’yan ƙasashen waje fiye da 53,000 zuwa ƙasashensu, inda ’yan Malawi da Zimbabwe
da Mozambique suka fi yawa.