Pep Guardiola na son sayo Dani Alves

An wallafa

Ga alama kociyan Manchester City Pep Guardiola zai nemi Juventus ta sayar wa kungiyarsa Dani Alves domin ya kara karfin bayansa.

A yanzu City ba ta da wani kwararren dan baya bayan da ta saki 'yan bayanta biyu Pablo Zabaleta da Bacary Sagna, wadanda kwantiraginsu da kungiyar ya kare.

A da dai ana rade-radin Guardiola zai dauko dan bayan Tottenham Kyle Walker ne amma kuma yanzu ana ganin yana duba yuwuwar sayo Alves, wanda ya yi wa Juventus wasa a lokacin rashin nasarar da ta yi da Real Madrid ta Kofin Zakarun Turai na bana a wasan karshe.

Ana tunanin Zakarun na Italiya na neman a ba su fan miliyan biyar kafin su rabu da Alves din dan Brazil mai shekara 34.

Guardiola ya san Alves sosai domin shi ya sayo dan wasan daga Sevilla a kan fan miliyan 23, ya kai shi Barcelona a shekarar 2008.

Tun daga lokacin tare suka dauki kofin La Liga uku da kofin kalubale na Spaniya biyu da na Zakarun Turai biyu, kafin Guardiola ya bar Nou Camp a 2012.