Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Messi ya ci kwallo 301 a La Liga a Nou Camp
An wallafa
Barcelona ta ci gaba da taka rawar gani a gasar La Liga, bayan da ta ci Eibar 6-1 a wasan mako na biyar da suka fafata a ranar Talata.
A karawar ce Lionel Messi ya ci kwallo hudu, sauran 'yan wasan da suka ci wa Barcelona sun hada da Paulinho da kuma Denis Suarez.
Eibar ta zare kwallo daya ta hannun Sergi Enrich a lokacin wasa ya koma 3-1.
Da wannan sakamakon Messi dan wasan tawagar Argentina ya ci kwallo tara a gasar La Liga, kuma guda 301 jumulla ya ci a Nou Camp a shekara 13 da ya yi a kungiyar.
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta ci wasa biyar tana da maki 15.