Napoli ba kanwar lasa ba ce - Pep Guardiola

An wallafa

Duk da cewar Manchester City ta doke kungiyar kwallon kafa ta Napoli 2-1 a Etihad ranar Talata a fafatawar da suka yi a wani wasan gasar zakarun Turai, kociya Pep Guardiola ya ce kungiyar ta Napoli ba kanwar lasa ba ce.

Guardiola ya jinjina wa kungiyar kwallon kafar da ke taka leda a gasar Serie A.

"Na sani kafin mu yi wasa da kuma bayan mun yi wasan cewa Napoli daya ce daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai," in ji Guardiola.

Ya kara da cewa: "Karawar da muka yi da su daya ce daga cikin fitattun wasanni.

"Na san kungiyar da muka doke. Kungiyoyin da suka kai matakinta ba cikin sauki ake doke su ba."