Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Unai Emery ya kare tsarinsa na sauya 'yan wasa
Unai Emery ya kare hukuncin da ya yanke kan canza dan wasa mai cin gwala-gwalai Alexander Lacazette bayan da Liverpool ta doke kungiyrsa inda kuma ta ci Fulham 4-1.
Dan kwallon wanda dan asalin kasar Faransa ne ya ci wa Arsenal kwallaye biyu kafin aje hutun rabin lokaci, in da aka canza shi da dan wasan tsakiya Aaron Ramsey, inda daga baya Aboubakar Kamara ya zura kwallo a minti na 69.
Wannan ya jawo bakaken maganganu daga magoya bayan kungiyar kwallon kafar.
"Na fahimci yadda magoya bayanmu suka ji" a cewar Emery, inda kungiyar kwallon tasa ta matsa maki biyu kusa da Chelsea wadanda su ne na hudu a teburin.
Arsenal ta sha kayi mafi girma a wannan kakar, inda Liverpool ta doke ta a ranar Asabar da ta gabata.