'Yan Barca 22 da za su kara da United

Barcelona
An wallafa

A ranar Laraba ne Barcelona za ta ziyarci Old Trafford, domin buga wasa da Manchester United a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

United za ta karbi bakuncin kungiyar ta Spaniya a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar ta Zakarun Turai ta Champions League.

Tuni kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 22 da zai je da su Ingila ranar Talata, domin buga karawar zagayen farko.

Kungiyoyin biyu sun fafata a gasar Zakarun Turai sau 11, inda Barcelona ta ci wasa hudu, United ta yi nasara a karawa uku da canjaras hudu.

'Yan Barcelona 22 da aka bayyana:

Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Todibo da Coutinho da Arthur da Suarez da kuma Messi.

Sauran sun hada da Dembele da Malcom da Lenglet da Murillo da Jordi Alba da Prince da Roberto da Vidal da Umtit da Alena da kuma Inaki Pena.

Sakamakon wasa hudu da suka kara a bayan nan:

Champions League 28 ga watan Mayu 2011

  • Barcelona 3 - 1 Man Utd

Champions League 27 ga watan Mayu 2009

  • Barcelona 2 - 0 Man Utd

Champions League 29 ga watan Afirilu 2008

  • Man Utd 1 - 0 Barcelona

Champions League 23 ga watan Afirilu 2008

  • Barcelona 0 - 0 Man Utd

Barcelona ta lashe kofin Champions League guda biyar, yayin da Manchester United take da shi guda uku.

Sai dai United tana ta shida a kan teburin Premier da maki 61, ita kuwa Barcelona tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki 11 tsakaninta da Atletico Madrid ta biyu.