'Yan Barca da suka fafata da Liverpool a Camp Nou

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta ziyarci Nou Camp ranar Laraba, domin buga wasan farko na daf da karshe a kofin Zakarun Turai na Champions League.
Tuni kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 18 da za su fuskanci kungiyar Anfield, a karawar da aka yi hasashen za ta yi zafi matuka.
Cikin 'yan wasan sun hada da Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Coutinho da Arthur da Suarez da kuma Lionel Messi.
Sauran sun hada da Dembele da Cillessen da Malcom da Lenglet da Jordi Alba da Roberto da Vidal da Umtiti da kuma Alena.
Har yanzu Rafinha na jinya, yayin da Todibo da Murillo da Boateng da kuma Vermaelen ba sa cikin 'yan kwallon da za su fuskanci Liverpool a Nou Camp.
A makon da ya wuce ne Barcelona ta lashe kofin La Liga na bana, kuma na 26 jumulla, inda Kyaftin Lionel Messi ya dauki na 10 a tarihi.
Barcelona na fatan lashe kofi uku, bayan da tauni ta lashe na La Liga za ta buga wasan karshe a Copa del Rey ranar 25 ga watan Mayu da Valencia.
Shin abin tambaya ko wannan karon Messi zai zura kwallo a ragar Liverpool?

Asalin hoton, Getty Images



























