Man City ta fi Man Utd daraja a kungiyoyin firimiyar Ingila

Manchester City
Bayanan hoto, An kiyasta City ta kai darajar fam biliyan 2.364
An wallafa

Kungiyar Manchester City ta sha gaban Manchester United bayan ta zama kungiya mafi daraja a gasar Firimiya, kamar yadda wani sabon nazari na Football Finance ya bayyana.

An kiyasta City ta kai darajar fam biliyan 2.364, yayin da United take a darajar fam biliyan 2.087, wato ta fado da fam miliyan 376.

Ana ganin hakan yana da alaka da "albashi mai kauri da kungiyar ke biya da kuma asarar da ta tafka."

A duka nazarin da aka yi a cibiyar kasuwanci ta Jami'ar Liverpool, an gawo cewa duka darajar lig din Firimiya yanzu ta kai fam biliyan 14.7 ya fadi da kaso 1.6 cikin 100.

City da United su kadai ne kungiyoyin da suka kai darajar fam biliyan 2 a wani nazari da aka yi a kakar wasannin 2017/18.

Tottenham ta kai fam biliyan 1.83, Liverpool fam biliyan 1.615, ita ma Chelsea fam biliyan 1.615, wannan babban ci gaba ne ga kungiyoyin, sai dai Arsenal ta yi baya zuwa fam biliyan 1.368 saboda ba ta buga gasar zakarun Turai.

Jami'ar ta tattaro wadannan bayannan ta lissafa kudaden shigar kungiyoyi, da ribar da suke samu, da ribar da suke samu ta sayer da 'yan wasa bayan shekara uku da suka gabata.

Da kuma kadarorin kungiyoyin, da albashin 'yan wasa, da yawan tikitin da suke siyarwa.

Binciken ya bayyana cewa, City tana matsayin farko ne saboda kudin shigar da take samu masu yawa, da kuma rashin biyan 'yan wasa kudi masu yawa, ta samu fam miliyan 39 a matsayin riba na kudin dan wasan da ta sayar a farkon kakar wasanni bara.

"Tsarin tafiyar da kungiyar wanda wanda ya mallaki kungiyar Sheikh Mansour yake tafiyar da kungiyar a kai ya sa ba a bin kungiyar bashi ko wanne iri, daga bangaren kudin ruwa ko kuma masu hannun jari a kungiyar."