Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Romelu Lukaku: Man Utd ta yi watsi da tayin £54m na Inter Milan
Manchester United ta yi watsi da tayin da Inter Milan ta yi wa dan wasan BelgiumRomelu Lukaku kan fam £54m
Inter dai ba ta taya dan wasan mai shekara 26 yadda Manchester United ta daraja dan wasan ba, wanda ya dawo Old Trafford shekaru biyu da suka gabata kan fam £75m.
Lukaku ba ya cikin 'yan wasan da suka buga wasan share fagen kaka da Inter, inda kocin kungiyar antonio Conte ya ce dan wasan shi ne na farko da zai saya.
"Ina masa kallon dan wasan da zai inganta tawagarmu," in ji Conte.
A ranar Juma'a Conte ya amsa cewa ya yi kokarin ya karbo Lukaku a lokacin da yana Chelsea tsakanin 2016 zuwa 2018.
"Ina kaunar dan wasan," a cewarsa.
Inter dai na son Lukaku ya maye gurbin dan wasan gabanta Mauro Icardi, wanda ya kauracewa wasannin share fagen kaka na kungiyar a yayin da rahotanni suka nuna zai tafi.
Lukaku ba da shi Manchester United ta buga dukkanin wasanninta na share fagen kaka ba a Australia saboda jinyar raunin da yake.
Sannan ba ya cikin tawagar da ta buga wasa a Singapore.
Kocin United Solskjaer, ya ce dan wasan na kokarin ya dawo taka leda saboda raunin da yake fama da shi.