Man United ta samo maki a Wolves

An wallafa

Manchester United ta samo maki daya a gidan Wolverhampton Wanderers, bayan tashi wasan Premier 1-1 karashen karawar mako na biyu ranar Litinin a Molineux.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Anthony Martial minti 27 da fara tamaula, kuma haka aka je hutu.

Bayan da aka dawo ne Wolverhampton ta farke ta hannun Ruben Neves minti na 10 da fara zagaye na biyun.

Dan wasan United, Paul Pogba ya samu fenariti da kansa, sai dai kuma ya buga ya barar.

A bara United ta kasa doke Wolves a wasa ukun da suka fafata, inda sau biyu ana doke United da ci 2-1 a filin wasa na Molineux.

Haka kuma a baran ne Wolves ta je gidan United wato Old Trafford ta yi kunnen doki 1-1 a gasar Premier, kuma Wolves ce ta fitar da United a FA Cup.

Kawo yanzu United ta hada maki hudu a wasa biyu, bayan da ta ci Chelsea a wasan makon farko 4-0 a Old Trafford.

Ita kuwa Wolves mai buga wasannin cike gurbin shiga gasar Europa ta bana tana da maki biyu a gasar Premier, bayan da wasan farko ta tashi babu ci a gidan Leicester City.

Ranar Asabar 24 ga watan Agusta za a ci gaba da wasannin mako na uku a gasar Premier, inda a ranar United za ta karbi bakuncin Crystal Palace, Burnley ta ziyarci Wolves.