Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal: An kori Unai Emery daga aikinsa
Freddie Ljungberg ya maye gurbin Unai Emery a matsayin kocin Arsenal na wucin gadi yayin da ta ce tana ci gaba da neman kocin dindindin.
Tuni Ljungberg ya fara jan ragamar tawagar a filin atasaye.
Arsenal dai ta bayar da sanarwar korar kocinta Unai Emery a yau Juma'a tare da dukkanin mataimakansa.
"Mun bayar da sanarwar cewa mun yanke hukuncin rabuwa da kocin tawagarmu Unai Emery da kuma mataimakansa," kungiyar ta bayyana.
Ta kara da cewa: "Muna godiya ta musamman ga Unai Emery da abokan aikinsa bisa jajircewarsu domin dawo da Arsenal kan turbar lashe kofuna kamar yadda muke bukata".
"Muna yi wa Unai fatan alheri a ayyukansa na gaba. An dauki matakin ne saboda irin sakamakon da aka rika samu wanda ba shi ne abin da ya kamata ba."
Gunners ba ta ci wasa ba a cikin bakwai da ta buga sannan kuma ta yi rashin nasara da ci 2-1 har gida a hannun Frankfurt a daren jiya a gasar Zakarun Turai ta Europa League.
Rabon da ta ci wasan Premier tun ranar 6 ga watan Oktoba kuma maki takwas ne tsakaninta da 'yan hudun farko a saman teburi.
"Muna da kwarin gwiwa kan Freddie Ljungberg domin ciyar da kungiyar gaba," in ji Arsenal.
"Muna ci gaba da neman koci sannan kuma za mu bayar da wata sanarwa a nan gaba."
Wadanda ake sa ran za su karbi aikin horar da kungiyar na dindindin sun hada da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino da mataimakin kocin Man City Mikel Arteta da tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri, sai kuma Eddie Howe kocin Wolves.
Arsenal ta kare a mataki na biyar a shekarar Emery ta farko bayan ya maye gurbin Arsene Wenger a watan Mayun 2018.