Odion Ighalo zai ci gaba da zama a Manchester United zuwa Janairu

Odion Ighalo
Bayanan hoto, Odion Ighalo ya ci kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa Manchester United
An wallafa

Dan wasan Shanghai Shenhua da tawagar Najeriya, Odion Ighalo ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da buga wasannin aro a Manchester United zuwa Janairun 2021.

Ighalo, mai shekara 30 ya je Old Trafford da taka leda a watan Janairu daga Shanghai Shenhua ta China kan kwantiragin karshen watan Mayu.

Kunshin yarjejeniyar da ya rattaba hannu a yanzu ta hada har da batun United za ta iya sayen shi na dundundun idan tana bukata.

Ighalo ya ci kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa United, har da wadda ya ci a Europa League a wasan da kungiyar Old Trafford ta ci LASK 5-0 ranar 12 ga watan Maris a Europa League.

Karawar ita ce ta karshe da United ta yi a bana, daga nan aka dakatar da dukkan wasanni saboda bullar cutar korona.

Ana sa ran ci gaba da gasar Premier League ta bana don karkare kakar 2019-20 daga 17 ga watan Yuni.

United tana ta biyar a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea ta hudu, kuma saura wasa tara a kammali Premier League ta shekarar nan.

Kungiyar da Solskjaer ke jan ragama ta kai karawar daf da na kusa da na karshe a FA Cup, za kuma ta buga wasa na biyu da LASK da ta ci 5-0 a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a Europa League.