La Liga: Madrid ta yi canjaras a gidan Real Sociedad a wasan farko

An wallafa

Real Madrid ta tashi wasa ba ci a gidan Real Sociedad a karawar farko da ta buga a kakar bana a La Liga.

Real Madrid wacce ta lashe kofin bara ta fara wasa latti a kakatr nan, bayan da ta fafata a gasar Zakarun Turai a watan jiya.

Ita dai Real ba ta samu damar maki da yawa ba a wasan, Karim Benzema ya samu wata dama ya buga kwallo amma Alex Remiro ya hana ta shiga raga.

Tsohon dan kwallon Manchester City, David Silva ya buga wa Sociedad karawar farko a kungiyar, sai dai bai bayar da kwallon da za a zura a raga ba.

Real Madrid ta saka sabon dan wasa Marvin Park a karawar a Sociedad wanda ya yi kaka uku a karamar kungiya mai suna Tranmere Rovers.

Real Madrid da Sociedad sun hadu sau uku a bara, inda suka fara a La Liga a Santiago Bernabeu, kuma Real ta yi nasara da ci 3-1 ranar 23 ga watan Nuwambar 2019.

Ranar 6 ga watan Fabrairun 2020 kungiyoyin suka gwabza a Copa del Rey, inda Sociedad ta samu nasara da ci 4-3.

Haka kuma sun kara haduwa karo na biyu a La Liga a gidan Sociedad ranar 21 ga watan Janairun 2020, inda Real ta ci 2-1.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 22 da za su buga karawar ranar Lahadi a gidan Sociedad.

'Yan kwallon da Real Madrid ta je da su Sociedad:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Mendy.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Odegaard da Marvin da kuma Arribas.

Masu buga gaba: Benzema da Mayoral da Jović da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.